Al'umma Sun Yi Jinjina Ga Matawalle Kan Aikin Ginin Hanya Da Ya Assasa Musu

YANCI HAUSA
By -
0


 Al'ummomin Dan Marke, Ruwan Dorawa Da Kanoma Sun Yi Jinjina Ga Matawalle Kan Aikin Ginin Hanya Da Ya Assasa Musu 


Kungiyar cigaban yankunan Dan Marke, Ruwan Dorawa da Kanoma, sun yi jinjina da yabo ga tsohon Gwamnan jihar Zamfara Dr Bello Matawalle da ya kammala aikin ginin hanyar da suka dade suna rokon a yi musu a lokacin yana Gwamnan jihar Zamfara.


Hanyar mai nisan kilomita 15 ta hada al'ummomin uku.


Kungiyar ta kuma caccaki Gwamnan jihar mai ci Dauda Lawan da suka yi zargin cewa ya yi watsi da su, ya gaza sauke nauyin al'ummar da ya dauka.


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Awwal Mohammed Dorawa da ya fitar a ranar Juma'a, kungiyar ta bayyana aikin ginin hanyar a matsayin wani gagarumin cigaban da zai tallafi yankin, da hakan zai inganta aikin gona da tsaron yankin.


"Tun shekarar 1999, babu wani tsohon Gwamnan da ya waiwayi al'ummar yankin ya kammala musu aikin hanyar. Amma Matawalle ya zo ya kammala musu aikin cikin kwanakinsa 100 na farko a matsayin Gwamnan jihar. In ji Ruwan Dorawa.


Kungiyar ta tabbatar da cewa aikin zai saukaka musu wajen sufuri da zai taimaka tattalin arzikinsu ya bunkasa kuma tsaron yankunan ya inganta. Sannan sun ce sun yi kewar jagoranci irin na Bello Matawalle, suke cike da rokon da ya dawo a matsayin Gwamnan jihar Zamfara a zaben 2027 mai zuwa. Suna masu nuna cikakken goyon bayansu ga Matawalle.


"Matawalle a lokacin yana Gwamna ya yi aiki tukuru don inganta harkar sufuri da kuma kyautata rayuwar al'ummar jiharsa ta Zamfara". In ji Ruwan Dorawa.


Matawalle da ya yi Gwamnan jihar Zamfara a shekarar 2019-2023, yanzu kuma shi ne Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya. Wa'adin mulkinsa ya taimaka sosai wajen inganta rayuwar mutanen jihar Zamfara. 'Yan kungiyar suka bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da ya fifita jin dadin jama'ar sa fiye ma da bukatar kashin kansa.

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)

#buttons=(Ok, Go it!) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn more
Ok, Go it!